Duk wani abu da ka ke gani a matsayin ICT ko SMC da mutane ke amfani da shi walau a kirifto ko forex, bisa nazari da bincike da na yi, na fahimta cewa kwafi ne ne Elliot Wave Theory.
Domin Ralph Nelson Elliot ne ya fara aiki na farko, sauran su ka biyo bayan sa. Kuma idan ka duba aiyukan su duka, za ka fahimta cewa galibin sauran aiyuka da su ka biyo baya, an gina su ne bisa fahimtar nazariyyar farko ta Elliot.
Kamar dai Satoahi Nakamoto ne a kirifto, duk wanda zai samar da wani kirifto, asalin babansa shine Satoshi. Domin shine ya sunnanta kirifto din.
Dabi'un kasuwa na market structure da m